Thursday

Home AN BINNE MUTANE 23 A KABARI DAYA A WANI GARI MAI SUNA CHAWAI A JIHAR KADUNA
Mutum 23 ne aka binne a wani kabari na bai-daya bayan wani rikici a gundumar Chawai ta jihar Kaduna a kwanannan.
Wadanda aka binnen na daga cikin mutane fiye da 30 da suka rasa rayukkansu a cikin rikicin wanda ya barke tsakanin manoma da makiyaya kan wata gona a gundumar wadda ke yankin karamar hukumar Kauru ta kudancin jihar.
Wadannan bayanan sun fito fili ne bayan da kwamitin wanzar da zaman lafiya a jihar ta Kaduna ya ziyarci yankin domin gane wa idonsa abin da ya faru.
Wani wakilin BBC da ya ziyarci yankin tare da tawagar kwamitin ya ce ko baya ga hasarar rayukka, tashin hankalin ya haifar da asarar gidaje kimanin 130.
ImageKaduna ta sha fama da rikice-rikice a baya  LIKE US ON FACEBOOK
ImageHukumomi sun sha alwashin daukar mataki
No comments:
Write Comments