Friday

Home GARABASA TUN A GIDAN DUNIYA

Wata rana Imamu Ahmad bin hambalI yayi tafiya
zuwa wani gari...
Inda ya tsinci kansha CIKAKKEN BAKO..
Duk da cewa sunan shi ya bazu a duniya; sai dai
ba kowa ba ne ya sanshi a fuska..
Saboda a wancan lokacin babu hoto..
Saboda haka ya sauka a wani masallaci...
Da dare yayi mutane suka watse, sai wani daga
cikin masu gadin masallacin ya nemi ya fitar
dashi..
Saboda dokar su ta hana kwana a masallaci...Sai
Imam Ahmad ya fito ya zauna bakin kofa...Mai
gadin nan ya Kara biyo shi yace lallai sai ya
tashi...
Da yaga imam ahmad zai bata mashi Lokaci, sai
ya kama kafarshi ya jawo shi har bakin hanya...
Dadai wurin da ya ajiye shi Akwai shagon wani
dattijo yana gasa gurasa...
Sai ya tausaya ma wannan bakon, ya bashi wuri
a shagon shi ya kwana...
Shi kuma ya cigaba da aikinshi, yana kwaba
filawa amma kuma bakin shi yana anbaton Allah:
*SUBHANALLAH
*WALHAMDU LIL LAH
*LAA. ILAHA ILLALLAH
*ALLAHU AKBAR
Haka ya cigaba har gari ya waye..
Imam Ahmad yayi mamaki, sai ya tambaye shi:
��Tun yaushe kake wannan azkar?
��Tun ina matashi na saba ma baki na da
anbaton Allah, sai Allah ya sauqaqa min Shi
kamar yadda nake numfashi..
��sai Imam Ahmad yace. To wane fa'ida ka
samu albarkacin wannan kyakkyawa aiki...
��babu abinda zan roki Allah ya hana ni..!
��yanzu duk abinda ka roki Allah ya baka!?
��kwarai kuwa, sai dai abu guda daya...
��sai Imam Ahmad yace menene shi?
��sai yace na roki Allah ya nuna min Ahmad
bin Hanbal, amma har yanzu ban amsa min
ba...ALLAHU AKBAR.........
Da imam Ahmad ya ji haka sai yace:
ALLAHU AKBAR, yau gashi Allah ya kawo ma
Ahmad har shagon ka ana janshi a kasa...
Ya Dan Uwa na Ban San wata falala da zaka
samu ba idan ka yawaita zikiri kuma ka tura
wannan sako ga abokai da yan uwa
Amma dai nasan annabi yace:
Wanda yayi nuni zuwa ga wani aikin alheri, yana
da kwatankwacin ladan Allah ya bamu ikon yin
aiki da umurni da aikin alkhairi Ameen
No comments:
Write Comments