Friday

Home Gaskiyar abin da yasa Atiku yake fada ga Gwamnan kaduna El-rufa'i
Malam Uba Sani ya bayyana abunda ya
haddasa babban gaba a tsakanin tsohon
ubangidansa, tsohon mataimakin
shugaban kasa Atiku Abubakar da
Malam Nasir el-Rufa’I, wanda a
karkashinsa yake aiki yanzu a matsayin
mai basa shawara a harkan siyasa.
Mataimakin na gwamnan jihar Kaduna,
a wani hiransa da yan jaridu a Abuja,
yace El-Rufai mutun ne mai gaskiya
kuma cewa wannan ya sa yana da
masoya da kuma makiya da yawa.

Sani ya bayyana cewa a baya, “ kokarin
ganin ya dukufar da el-Rufai ta ko halin
‘ka’ka ya kasance abu mafi soyuwa ga
Atiku. Amma a matsayin mutane masu
hikima, zamu iya cinkar dalilin da yasa
yake yawan kai hari ga gwamnan a kai-
a kai.
Mataimakin gwamnan ya yi jayayya
cewa Mallam el Rufai bai taba
kasancewa mamba na tawagar yan
rashawa ba.
Na karanta hirar Alhaji Atiku da aka
buga a majullar Zero Tolerance, wanda
babu shakka aka kuma buga su a
dandamalin watsa labarai daban-
daban.
A cewar Sani, “Bajintar Mallam el Rufai
a dukkan mukaman da ya rike sanannu
ne kuma an ajiyesu yanda ya dace. Yaki
da rashawarsa na saka shi cikin hatsari
a ko yaushe.
El-Rufai da muka sani ba zai taba karya
doka ko a kan kansa ba. Imma a inda
yayi aiki a matsayin Darakta Janar na
tsawon shekaru hudu; ko kuma a
ma’aikatar babban birnin tarayya, inda
yayi shugabanci a matsayin minister na
wani shekaru hudun; har ma a jihar
Kaduna inda yake a matsayin gwamna
mai ci, yaki da cin hancin el-Rufai mai
dorewa ne."
No comments:
Write Comments