Tuesday

Home HIKAYAR BIRNIN DUWATSU 01
Wata rana Halifa Haruna Rashid na duba harajin da sarakuna da hakimansa suka aiko da shi cikin wannan shekara, sai ya lura cewa Sarkin Basara ne kadai bai aiko da nasa harajin ba. Don haka sai Halifa ya tara 'yan majalisarsa. Da suka taru sai ya ce, "Ina Waziri Ja'afaru?" Waziri Ja'afaru ya zo kusa ga Halifa ya tsaya ya ce, "Ga ni, Allah ya daukaki mulkinka." Halifa ya ce, "Harajin kowane sarki da ke karkashina ya shiga baitulmali, amma babu harajin Basara." Ja'afaru ya dukar da kai ya ce, "Ya Shugaban Muminai, watakila akwai wani babban al'amari da ya faru ga Sarkin Basara da ya sa shi sha'afa da aiko da nasa harajin." Halifa ya ce, "Yau kwana ashirin da gama tattara haraji, idan har wani al'amari ya same shi, mi ya sa bai aiko mana ba, domin mu san halin da yake ciki?" Waziri ya amsa masa, "Allah ya taimake ka, ina ganin mu aika masa da manzo wanda zai dawo mana da labari." Halifa ya ce, "Ka tura Abu Is'haka al- Mausili, daya daga cikin amintattunmu." "Na ji, na amince.Ina mai biyayya ga Allah, ina mai biyayya gare ka, ya Shugaban Muminai." In ji Ja'afaru. Nan da nan sai Ja'afaru ya sa aka kira masa Abu Is'haka zuwa gidansa. Da ya zo sai ya rubuta takarda a madadin Halifa, ya ba shi ya ce, "Karbi wannan takarda ka kai wa Abdullahi dan Falilu, Sarkin Basara. Halifa ya duba dukkan harajin da sarakunansa suka aiko amma bai ga na Sarkin Basara ba. Idan ya tattara harajin ka karbo ka dawo mini da shi, idan kuwa bai tattara ba, to ka zo tare da shi, ya fada wa Halifa da bakinsa abin da ya hana shi aiko da nasa haraji." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na amince." Waziri Ja'afaru ya hada shi da mahaya dubu biyar suka nufi Basara. Yayin da suka yi kusa da birnin Basara sai Abdullahi dan Falilu ya sami labarin zuwansa. Nan take ya fita da runduna ya tarye shi, suka dawo cikin birni tare, har suka isa fada. 'Yan rakiya kuma sai suka kafa tantuna a bayan gari, aka aika musu da dukkan abin da suke bukata na abinci da abin sha da shimfidu.Lokacin da Abdullahi dan Falilu da Abu Is'haka suka shiga fada, sai Abu Is'haka ya zauna bisa karaga, ya zaunar da Abdullahi dan Falilu kusa gare shi. Wazirai da fadawa kowa ya zauna gwargwadon matsayinsa. Da fada ta nutsu, sai Abdullahi dan Falilu ya mike. Bayan ya yi sallama da gaisuwa ga Abu Is'haka sai ya ce, "Ya shugabana, ko akwai wani sako ne da ka zo mana da shi?" Bako ya amsa, "I. Na zo ne domin na karbi harajin kasarka. Kowa ya aika da harajinsa amma Halifa bai ga naka ba, ga shi har lokacin karba ya wuce." Abdullah dan Falilu ya yi murmushi ya ce, "Allah Sarki, an ce rashin sani ya fi dare duhu. Da ka sani da ba ka walar da kanka garin zuwa ba. Haraji na nan na kammala hadawa, da gobe nake niyyar aikawa da shi. Amma tun da ka zo zan damka shi ga hannunka, ka wuce wa Halifa da shi. Yanzu sai ka zauna ka huta zuwa kwana uku, mu shirya maka liyafa ta musamman domin karramawa da kuma girmama Halifa, a kwana na hudu sai na ba ka harajin tare da tsarabar da za ka tafi da ita." Abu Is'haka ya ce, "Babu laifi ga wannan." Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya sallami kowa. Da aka watse sai ya ja bakonsa zuwa wani kayataccen soro da babu kamarsa ga kyawu. Ya sa aka jera akussan abinci domin Abu Is'haka da manyan na hannun damarsa. Suka ci suna raha har suka bankare cikannansu. Da suka koshi sai aka kawar da akussa aka jera gorunan gahawa da abin sha. Suka yi ta sha suna hira, ba su ankara ba har dare ya raba. Aka shirya wa Abu Is'haka shimfida mai taushi bisa gadon zumarrazi da aka shafe da ruwan zinariya mai kyalkyali. Abullahi dan Falilu ya kwanta kusa gare shi, amma a nasa gadon daban. Abu Is'haka ya kwanta kamar zai yi barci amma barcin bai dauke shi ba. Sai ya yi ta karatu a cikin zuciyarsa, wani lokaci kuma sai ya rera baitoci a kan sha'anin rayuwa. Da ma shi mutum ne gwanin hikima, ga shi kuma gwanin bayar da labari, shi ya sa Halifa ke son sa kwarai da gaske har ya sanya shi daya daga cikin amintattunsa. Haka ya ci gaba da karatunsa yana rera wakoki har zuwa talatainin dare....

KU KASANCE TARE DAMU DON CIGABA.
GASKIYA DA GASKIYA BA MAGANAR YAUDARA DA FATAN ZAKU FAHIMCE NI.
No comments:
Write Comments