Sunday

Home KWASTAM NA SHIRIN KARA HARAJIN SHIGAR DA MOTOCI NIGERIA.
Hukumar kwastam a Najeriya na shirin yin karin kudin haraji akan motocin kawa da ake shigowa da su daga kasashen ketare, a cewar wata majiya kwakwkwara.

Karin wanda ake shirin sanarwa zai kai kashi dari-bisa-dari akan motocin kirar Jeep-jeep kamar yadda majiyar wacce ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatarwa Sashen Hausa na Muryar Amurka.
Wannan sabon mataki da hukumar ke shirin dauka na zuwa ne makwanni biyu da sanar da shirin hana shiga da motoci ta kan iyakokin kasar.
Ana sa ran shirin na hana shiga da motoci zai fara aiki ne nan da daya ga watan Janairun shekara mai zuwa.
Hukumar kwastam din ta yi korafin cewa Najeriya na rasa makudan kudaden haraji idan ana shigar da motocin ta kan iyakokin kasar.
A makon da ya gabata Majalisar dokokin kasar ta bukaci a dakatar da shirin, wanda ta ce zai jefa dumbin 'yan Najeriya cikin kangin rashin aikin yi.
Kwatsam kuma sai ga wannan mataki na karin haraji kan motoci kirar Jeep da ake shirin sanarwa.
“Tsarin haraji ya na sa gwamnati ta samu kudi amma kuma ya na sa mutane cikin tsanani.” In ji Malam Lawal Habib na kwalejin Fasaha ta Kano.
Kokarin jin ta bakin hokum at ta kwastam dangane da wannan shiri ya cutura.
Domin jin cikakken rahoto kan wannan lamari, saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:
No comments:
Write Comments