Tuesday

Home MAJALISSAR DINKIN DUNIYA (united nation) TA YI SABON SHUGABA

A jiya ne aka rantsarda Antonio Guterres na kasar Portugal a matsayin sabon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD a takaice.

A jawabinsa na kama aiki, sabon sakataren yace MDD na bukatar ta rage “dogon turanci”, ta fi maida hankali wajen “cika aiki.
Shi dai Guterres, 67, wanda tsohon frayim-ministan Portugal ne kuma tsohon shugaban cibiyar kula da ‘yan gudun hijira na MDD, ya kada mutane 12 ne a gasar neman wannan mukamin.
Ganin irin matsalolin da duniya ke fuskanta, wadanda suka hada da kalubalen ‘yan gudun hijira, yake-yake a kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da na Afrika, barazanar ta’addanci da maganar chanjin yanayi, ana ganin cewa sabon sakataren na da aiyukka da yawa da zasu dauke mishi hankali na wani lokaci mai tsawo bayan ya karbi aikin daga hannun sakatare mai barin gado, Ban Ki-moon a ran 1 ga watan Janairun sabuwar shekara.

latsa wannan link don ganin hotunan Sabon shugaba Antonio.

http://appsource.wapka.mobi/site_2.xhtml/

No comments:
Write Comments