Friday

Home SAKO DAGA SHAIDAN ! !! !!! !!!! !!!!!
SAKO DAGA SHAIDAN !!! : Barkanku da warhaka! Sunana Iblis dan Lis (SHAIDAN), Jagoran masu sharholiya da sheke ayarsu, Na girmi mahaifin 'Yan Adam balle Annabawa da Manzanni, na kuma zauna acan Sama, yau kuma gani a kasa, na shiga Aljanna na kuma ga wuta da idona, Saboda haka ban ga abin tsoro ba, don mu muka san Jiya balle Yau. : Na san ana fada muku cewa ni Makiyinku ne ko??? Amma yaya makiyinku zai nusar da ku kan abinda zai sanya rayuwarku anan Duniya cikin Holewa da morewa da fantamawa ??? Ina kiranku ku biyoni muci Duniyarmu da tsinke!! : Na san abinda ake tsorataku da shi itace Wutar Jahannama, To ai Manzon Allahh (s.a.w) yace cikin Mutum dubu daya ne kawai zai shiga Aljanna, Jahannama mai tsallaketa a wannan Zamanin 'yan kadan ne!! : Shedan yaci gaba da cewa ''Kar ku damu abin Ruwan dare ne, kuma gobara ce a kasuwa. : Ina kira ga Mata manyan kwamandojina, Da ku kara himma, ku samo mana mabiya, don ina alfahari da kokarinku na samo abokan zama a wuta, sama da kokarin sauran tawagata, Ku rudesu ku batar da su, kuyi shigar ashararanci, Ku dauke musu hankali, Sannan ku kuma ku sheke ayarku a gidajen Biki, kar ku kyale lokacinku ya amfaneku, ga Kalle-kalle don nishadantarwa, ku bata lokacinku a kansa, Naji ance wani sabon kaset ma ya fito ko haka kuma akwai sababbin dinku masu danbanzan kyau da nuna surar jiki, maza garzaya ki mallaki naki don ganin kinci moriyar kuruciyarki?? : Malaman Bidi'a da 'yan tsubbu da masu addu'ar sayarwa, na san ana kokarin bata tsakanimmu, wai kuma na Allah ne, Kar ku damu!! Ni nasan gudummawar dakuke bayarwa kan wannan Tafiya ta fi gudummawar masu gidan Giya da mafi yawan Mabarnata, domin hanyarku da wahala a tuba, Gani ma ake yi bautar Allah kuke yi, don na riga na kawata muku wannan turba, sannan ga wahayin rubabbun hujjoji da na ke muku a koda yaushe, amma sauran masu sabo sai kaga mutum ya jima ana gwagwarmayar nan da shi, sai kaji kwatsam wai ya tuba!! Amma ku kam da wahala irin haka ta faru domin baku jin cewa zunubi kuke aikatawa. Kar ku damu, In munje Lahira kuce ni na batar daku, Na dauka muku alkawarin baku kowace irinkariya, sai dai in wuri yayi wuri zan ce ban taba saninku ba, In Lamari yayi tsanani, wiri yayi wuri, Iya ruwa ne fidda kai!! : A karshe kun san ai makomarmu dai wuta ne ko? Na kuma san bamu da rabo a lahira, amma kam!! Ai muna sheke ayarmu anan Duniya gabanin muje can Lahira a shigar damu wuta. Daga Makiyinku abokin gabarku Iblis wanda kukafi sani da SHAIDAN. ............................ KUKAN KURCIYA DAI AKACE JAWABINE. Allah ya tsaremu daga cikin mabiya Shaidan.
No comments:
Write Comments