Monday

Home YADDA AKE NEMO TSOHON LABARI KO TSAFFIN HOTUNA A SHAFIN FACEBOOK

Yadda zaka iya saukowa da dukkan bayanan da ka taba sanyawa kan shafinka na Facebook a kwamfutarka.

Idan mai sauraro kamar ni yake, na tabbata ya sanya hotuna marasa iyaka, da sakonni, da bayanan halin da yake ciki, da gaishe gaishe ko wasiku ga abokai na Facebook a cikin ‘yan shekarun da suka shige. Wasu ma ka rig aka manta da su kwata kwata. Har irin sakon nan da ka taba aika ma wata budurwa, ko kika aika ma saurayi. Idan kana son kwafe ko sauko da dukkan bayanan da ka taba sanyawa a shafinka na Facebook, to ga yadda zaka yi.
Da farko, zaka shiga cikin shafinka na Facebook, amma a kwamfuta ba ta cikin wani APP na way aba. Idan a way ace, sai ka bude manhajar shiga intanet, ko BROWSER, ka shiga, sai ka je ka kasa inda aka sanya VIEW FULL SITE ko kuma VIEW DESKTOP SITE, ka shiga.
Idan ka shiga sai ka duba can sama a kuryar hannun dama, zaka ga wata alamar kan kifiya mai kallon kasa, sai ka matsa. Idan ka matsa zai bude maka shafi dauke da zabin wasu abubuwa da zaka iya yi ko gani. A cikinsu sai ka matsa inda aka rubuta SETTINGS
A kasa a cikin shafin da zai bude bayan an matsa SETTINGS, za a ga wani wurin da a turance aka ce “DOWNLOAD A COPY OF YOUR FACEBOOK DATA.” Watau yi kofe na bayananka dake kan Facebook a Hausance. Sai a matsa daidai inda aka rubuta DOWNLOAD A COPY din. Idan an yi haka, wani shafin zai bude, wanda a cikinsa kuma sai a matsa inda aka rubuta “START MY ARCHIVE” a tiurance. A lura cewa wannan shafin zai nuna maka irin abubuwan da zai sauko maka da su, watau abubuwan da zai yi maka kofe a kwamfutarka, wanda ya hada da hotuna, bidiyo, sakonni, chat da duk abinda ka taba yi tun daga ranar da ka bude shafinka na Facebook.
Daga nan zshafin na Facebook zai tattara bayananka. Wannan watakila zai dauki lokaci mai tsawo idan har mutum ya jima yana sanya abubuwa kan Facebook. Bayan y agama tattara su, to facebook zai aika maka da wani sako ta Email cewa ya kammala tattara bayananka, yana bukatar ka tabbatar da cewa lallai kai din ne mai wannan shafi ta hanyar yi maka wasu tambayoyi da kai kadai zaka iya sani.
Daga nan sai ka zabi inda zaka ajiye wadannan bayanan a kwamfutarka. A yi hattara sosai domin watakila bayanan suna da matukar yawa. Idan mutum bay a da wadataccen wurin ajiyewa a kwamfuta, to kwamfutar na iya yin rauni, ko kuma ba ma zai iya ajiye komai ba.
A kuma lura da cewa, zai tattara bayanan ne ya tura maka su cikin irin manhajar nan mai takura bayanai ta rage musu nauyi, watau ZIP. Don haka kana bukatar wata manhajar a kwamfuta dinka wadda zata iya bude irin wadannan bayanai na ZIP.

Ziyarci babban shafin mu

No comments:
Write Comments