Monday

Home Zai yi wuya a samu gwamnatin Musulunci a Najeriya - Sheikh Sani Saleh Zariya
Saleh Zariya: Tunda farko mun kafa wannan kungiya ta Rasulul A’azam a shekarar 2003 inda muka yi mata rajista a shekarar 2005 da Hukumar CAC. Tana da manufofi uku isar da sakon ’ya’yan gidan Annabi Muhmmad (SAW - Ahlul Bait) na zamantakewa ta addini da abin da ya shafi rubuce-ubuce da bude makarantu da masallatai don ilimintarwa. Muna da cibiyoyi masu yawa a kusan duk fadin kasar nan, wuraren da ba mu da cibiya muna da wakilai a wurin.
Aminiya: A kwanan nan Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana bangaren Shi’a na IMN a matsayin ’yan ta’adda me za ka ce a kan haka?
Saleh Zariya: Ni a wurina ban dauke su a matsayin ’yan ta’adda ba, watakila ko don ban fahimci kalmar ba ne? Sai dai kowace kungiya ta addini za ta iya zama hakan, ma’ana za ta iya farawa da wani uslubi mai kyau a karshe ta kare da wani abu na daban saboda wasu dalilai a ciki da wajen kungiyar. Watakila ita Gwamnatin Jihar Kaduna tana da wasu bayanai ko hujjoji da ya sa ta fadi hakan. Amma ni wurina ba na kallonsu a haka.
Aminiya: Mene ne bambancinku da wancan bangare na Shi’a?
Saleh Zariya: Kowace kungiya ta addini idan an duba za a ga akwai bambance-bambace a taskaninsu, idan muka dauki Izala za mu ga cewa akwia Izalar Kaduna akwai ta Jos, haka abin yake a dariku idan ka dauki darikar Tijjaniyaya za ka samu akwai Faida akwai ’yan hakika da sauransu. To mu ma haka abin yake a cikin Shi’a. Idan kika dauki bangarenmu na RAAF ta tafi ne a kan akida ta koyarwar ’yan gidan Ananbi (SAW) ta yadda za a fahimce su. Mun zo mun samu wasu ’yan kungiya a kasar nan wato ’yan Harka ana kiransu da ’yan Shi’a saboda goyon bayansu ga kasar Iran. A wancan lokaci su akansu ba su amsa sunan ’yan Shi’ar sai a tsakiyar shekarun 1990 sannan suka karbi mazahabar Shi’a ta fuskar akidarsu da shugabancinsu, duk da cewa dai ba za a rasa daidaiku a cikinsu da ke bin tafrkin Shi’ar ba tunda farko. Mu kuwa dama tun daga ranar da muka fara wanann tafiya muka bayyana kanmu a matsyain ’yan Shi’a, inda muka nuna ita ce a kidarmu kuma ita za mu yada. Yawancinmu mun dawo daga karatu inda muka kwashe shekaru muna neman ilimi a kan wannan mazhaba ta Shi’a a Barkumul Ilmi, saboda a lokacin akwai mutanen da suke kan wanann mazahaba a kasar nan wadanda kuma ba su da ilimin Shi’ar. A duniya duk abin da mutum zai yi idan ba ya da ilimi a kai, to za a samu kura-kurai. Sun zama ’yan Shi’a ne ta hanyar karance-karance, wanda a yanzu ba abu ne mai wuya ka samu wasu tunane-tunane ta hanyar kafofin sadarwa ba.
Mun samu a kasar nan ana daukar Shi’a a (matsayin) wasu mutane da ba su yarda da Manzon Allah (SAW). Wasu mutane da ba su yarda da Alkur’ani ba. Wasu mutane da ba su da aiki sai kafirta Shababai da zagin matan Manzon Allah SAW). Haka kuma ana daukar su wasu mutane da ke halatta zina da kuma musayar mata. Wadannan dalilai ya sanya wasunmu muka zurafafa karatu don sanin ainihin mazhabar Shi’a. Misali ni sai na ji ina so in gano gaskiyar lamarin don in fadakar da jama’a a kai amma da na gudanar da bincike sai na gano ashe Shi’a daban wannan abubuwa da ake yadawa game da Shi’ar dban. Babu wata kungiya da ake yada maganaganun karya game da ita kamar Shi’a a shekarun baya. Sai dai alhamdulillah a yanzu da mutane suka fara iliminta sun gano cewa al’amarin ba haka yake ba.
Don mu wanke wa Shi’anci daga wadannan zarge zarge, ya sa muka zurfafa bincike tare da karantar da al’umma a kan haka. Sai muka samu cewa watakila masu wancan tunani suna yin wadanan abubuwa bisa kuskure ko wasu ke amfani da hakan don su samu abin fadi a wajen wa’azi. RAAF ba mu fitowa kan titi mu yi zanga-zanga. Akalla ba mu fitowa muna yaki da tsarin mulkin kasa. Muna shiga siyasa a cikinmu akwai wadanda suka tsaya takara. Kai da kanmu mun fito kafafen watsa labarai mun yi umarni ga jama’armnu su fita a yi zabe. Ba mu yi imanin cewa wata akida ta mayar da wani mutum bare ya zama a gefe, matukar shi dan kasa ne ba. Mu iyakar fahimatarmu da Shi’anci shi ne wasu abubuwa wajibi ne mutum ya fita ya aikata su, misali batun zabe da sauransu. La’alla wasu su yi mamakin hakan, ganin cewa a shekarun baya daya banagren na Shi’a ba a ganinsu a cikin makamantan wadannan abubuwa misali harkokin zabe da sauransu.
Mun yi imani da tsarin mulkin kasa da shugabancinta. Zuwa yanzu hukumomi da dama a kasar nan sun fahimci cewa akwai wani bangare na Shi’a da suke son ci gaban kasa da kuma hadin kanta. Kuma mu ba wata gwamnati da za ta ce muna zuwa wurinta neman gudummawa duk wani abu da za mu gudanar da ya shafi tattaunawa a kafafen watsa labarai da abubuwa na tuntubar juna duk muna yi ne cikin dan abin da Allah Ya hore mana.
Duk harkokinmu muna sanya gwamnati a ciki, tun daga kan bude makaranrtarmu da masallacinmu mun gayyaci shugabannin al’umma da suka hada da bangaren gwamnati da masarauta da sauransu. Idan muka samu wata rashin jituwa muna kaiwa gaban hukuma, don ban mantawa akwai rashin fahimta da ta bulla tsakaninmu da bangaren Harka, haka muka dauki maganar muka kai gaban ’yan sanda inda aka sasanta.
Duk da cewa a lokuta da dama daya bangaren na Harka ba su so muna bayyana bambance-bambancen da ke tsakaninmu, sai dai a lokacin da muke kokarin bayyana manufofinmu ba yadda muka iya mukan bayyana sabaninmu. Amma dai su Harka (IMN) su ya kamata su fito su fadi abin da suka yi imani da shi da kuma manufofinsu.
La’alla mutane ba su tunanin cewa akwai wasu ’yan Shi’a da ke da irin wadannan manufofi. A ka’ida ko dai hukuma ta zama ta Musulunci ko kuma ta zama ta jama’a, to a Najeriya muna da hukumar jama’a ce. Babu yadda za a yi mutum ya ce zai zo ya kafa gwamnatin Musulunci a kasa irin Najeriya mai mabambantan addinai da kabilu. Abu ne da ba zai yiwu ba. Ina ganin irin wadannan abubuwa ne ya kai wancan bangare na Harka Islamiyya inda suka samu kansu a cikin jarrabawar da ta fada musu a watan Disambar bara har ta kai shugabansu da matarsa suke a hannun hukuma, wanda a yanzu ake kan tattaunawa, muna yi musu fatan alheri, don a samu tattaunawa ta alheri.
Aminiya: Shin ana samun mutanen bangarenku suna komawa can bangaren ko kuma su ma suna komowa naku?
Saleh Zariya: A gaskiya ba zan iya fadin hakan ba, kasancewar ni ban taba gani ba, sai dai da yake idan mun tashi k mukan bude kofa ga kowa kuma mun san mutanensu sukan halarci majalisinmu, to amma ba za mu iya daukar hakan a matsayin sun dawo cikinmu ba. Watakil ko don ba manyan cikin nasu ba ne ke dawowa ko namu shi ya sa ba za mu iya sanin hakan kai-tsaye ba. Babu mamaki a iya samun haka, don dabi’a ce ta dan Adam. Abubuwa da dama sun hada mu, duk da cewa akwai bambance-bambance a tsakaninmu, to hakan ya sa muna haduwa mu yi abubuwa tare. Sai dai duk wanda zai shigo cikinmu muna yi masa maraba.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga al’umma?
Saleh Zariya: Kirana guda biyu ne, na farko ga al’ummar Musulmi gaba daya cewa abin da yake gabanmu ya wuce batun bambance-bambancen da ke tsakanninmu. Kowa yana sane da yadda aka sako Musulunci a gaba, don haka fatarmu ita ce Musulmi mu hada kai mu tunkari abin da ke gabanmu. Rarrabuwarmu ba za ta yi kyau ba a halin da ake ciki, mu ’yan Shi’a ’yan uwansu ne Musulmi mun mika musu hannu su zo mu taimaki addini Musulunci. Haka kuma ina kira ga ’yan kasar nan da mu zauna lafiya da juna, domin a duk lokacin da ake cikin tashin hankali, to fa babu natsuwar da za a yi batun bambamcin mazahaba ko kungiyar addini.
No comments:
Write Comments