Monday

Home › › Damisa ta cinye wani mutum har lahira
Damisa ta cinye wani mutum da ya shiga dakinta a wani gidan namun daji da ke gabashin kasar China.

Wasu jami'an tsaro na musamman dai sun harbe damisar har lahira bayan ta cinye mutumin ranar Lahadi a gidan namun dajin Youngor da ke birnin Ningbo.

An garzaya da mutumin, wanda ba a fadi sunan sa ba, zuwa wani asibit inda ya cika.
Har yanzu dai ba a san dalilin da ya sa mutumin ya shiga dakin damisar ba. Ana gudanar da bincike kan lamarin.
An rufe gidan namun dajin bayan aukuwar lamarin. Gidan talabijin mallakin gwamnatin kasar CCTV ya ce ba za a bude gidan namun dajin ba ranar Litinin.
Damisar ta rika cin mutumin ne a bainar jama'a, wadanda wasu daga cikinsu suka rika daukar hoton bidiyon abin da ke faruwa.


dannan wannan link din don samun rubutunmu a kullum

No comments:
Write Comments