VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Friday

Home Hatsarin Mota ya kashe Mutane Uku a Jihar Osun : HAUSAPOST28
Wani hadarin mota da aka yi a jihar Osun yayi sanadiyar asarar rayukan mutane uku da kuma raunata mutum guda. Kwamandan hukumar kiyaye faruwar hadura ta jihar Osun. Alhaji Umaru Ibrahim, shine ya tabbatar da faruwan hadarin, inda yace ya faru ne kan hanyar dake tsakanin mahadar Iwara zuwa garin Ibeto. Ya kara da cewa kasancewar yanayin kyawun hanyar yasa ake yawan samun hadura masu yawa. Cikin mutanen da suka mutu a wannan hadari sun hada da maza biyu da mace ‘daya. Gudu da motocin biyu ke yi da ya wuce kima shine yayi sanadin taho mu gama. Daga karshe Alhaji Umaru Ibrahim, yayi kira ga jama’a da rinka kula yayin tafiya kan wannan hanya, kuma idan direbobi na guda alhaki ya rataya kan fasinjoji da su yi musu magana don su rage gudu domin kiyaye faruwar hadari da salwantar rayuka.
No comments:
Write Comments