Sunday

Home HIKAYAR BIRNIN DUWATASU 04
Halifa ya yi murmushi ya ce, "Idan na aika wani zai iya musantawa ya ce, 'ni ba ni da wasu karnuka,' amma idan kai ka tafi ka ce masa, 'na gan su da idona' ba shi da ikon musantawa. Don haka dole kai za ka tafi ka zo mini da shi da karnukan nan, idan kuwa ba haka ba ina yanka ka." Abu Is'haka ya ce, "Na ji, na dauka, ya Sarkin Musulmi, Allah ya agaje mu. Da ma an ce harshe shi ke yanka wuya. Laifina ne da na gaya maka wannan labari, amma ina so ka rubuta mini takarda da hannunka wadda zan ba shi."

CIGABA....


Halifa ya rubuta takarda ya ba shi, ya karba ya kama hanyar Basara. Yayin da Sarkin Basara ya ga ya komo nan da nan, sai ya ce, "Allah ya sa dai lafiya ka koma haka da wurwuri, ya Abu Is'haka? Ko harajin ne ya yi kadan Halifa ya ki karba?" Abu Is'haka ya dube shi cikin jin kunya ya ce, "Ya Sarki Abdullahi, harajinku ya cika daidai, Halifa ya karba cikin farin ciki. Amma ka gafarce ni saboda na ci amanar bakunta, wannan kuwa sharrin Shaidan ne!" Abdullahi ya tambaye shi cikin mamaki, "Wace amana ka ci tamu?" "Ka sani kwana uku da na yi tare da kai, a cikin kowane dare nakan bi bayanka, ba tare da ka sani ba, har zuwa dakin da kake bugun wasu karnuka biyu. Wannan al'amari ya sa ni mamaki matukar mamaki, ni kuma sai na ji kunyar na tambaye ka. Yayin da na koma Bagadaza sai kaikayin baki ya ja ni, na gaya wa Halifa wannan labari. Da na san zai nemi na dawo na tafi da kai tare da karnukan da ban gaya masa labarin ba, to amma kaddara ta riga fata, babu wanda ya isa ya canja kaddarar Ubangiji.Ga takarda Halifa ya ce a ba ka, a ciki yana umurtarka da ka tafi gare shi tare da karnukan nan. Amma don Allah ka yafe mini wannan laifi da na aikata maka." Ya duka ya yi ta ba shi hakuri. Abdullahi ya yi jugum yana tunani, can sai ya ce, "Babu komai da yake kai Halifa ya turo ba zan iya karyata ka ba, domin kai abokina ne. Amma da a ce wani ne ba kai ba, ya fada wa Halifa wannan labari, da na musanta wannan al'amari, na ce wa Halifa karya yake yi, ni ba ni da wasu karnuka. Amma yanzu zan dauki karnukan mu tafi tare ko da hakan zai zama karshen rayuwata." Abu Is'haka ya kama hannun Abdullahi ya sumbata yana cewa, "Allah ya rufa maka asiri kamar yadda ka rufa mini asiri ba ka karyata ni ga Halifa ba." Abdullahi ya shirya tsaraba mai kauri da zai kai wa Halifa, ya dauki karnuka tare da shi, ya aza kowanne bisa rakumi ya daure shi da sarkar zinariya, ya tafi tare da Abu Is'haka har suka isa Bagadaza gaban Halifa. Abdullahi ya dauki kasa a gaban Shugaban Muminai, ya umurce shi ya zauna.Da ya zauna sai ya jawo karnukan nan biyu gaban Haruna Rashid, wanda ya tambaye shi, "Mene ne labarin wadannan karnuka, ya Sarki Abdullahi?" Karnuka kuwa sai sumbatar kasa suke yi gaban Halifa suna kada wutsiya kamar masu kawo kara gare shi. Halifa ya cika da mamaki, ya dubi Abdullahi ya ce, "Gaya mini labarin wadannan karnuka da abin da ya sa kake bugun su kowane dare, sa'annan kuma ka ba su abinci kana rarrashi." Abudllah ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjini da daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya....

BARKA DA SABUWAR SHEKARAR 2017Abdullahi ya dukar da kansa kasa a gaban Halifa ya ce, "Ya Halifan Allah, wadannan ba karnuka ba ne face samari biyu, ma'abuta kyawu da cikar halitta da kwarjini da daidaito. Su biyun nan duka 'yan uwana ne, uwarmu daya ubanmu daya." Halifa ya tambaye shi cikin mamaki, "Yaya dan Adam zai koma siffar kare?" Abdullahi ya amsa, "Ka yi mini izini, ya Shugaban Muminai, in labarta maka da gaskiyar labarinsu" Halifa ya ce, "Fada mini labarinsu, amma na hore ka da ka gaya mini gaskiya domin ita ce jirgin tsirar kowane mutum, ita ce alamar managarta daga cikin mutane." Abdullahi ya ce, "Ya Halifan Allah bisa ga bayan kasa, zan fada maka gaskiya a gaban wadannan karnuka, idan na yi gaskiya za su shaide ni, idan kuma na yi karya za su karyata ni a gabanka." Halifa ya dube shi, "Wadannan ai karnuka ne, ta yaya za su yi magana balle su gasgata ka, ko su karyata ka?" Abdullahi ya dubi karnuka ya ce, "Ya 'yan uwana, idan na fadi karya ku rauda kawunanku kuna kyibta idanu. Idan kuma na fadi gaskiya ku sunkuyarda kawunanku kasa kuna lumshe idanu." Daga nan sai Abdullahi dan Falilu ya fara labari ya ce, ya Halifa, ka sani mu uku muke 'yan uwan juna, uwarmu daya, ubanmu daya. Sunan mahaifinmu Falilu. An rada masa wannan suna ne saboda su biyu uwarsu ta haife su tare, 'yan tagwaye. Daya ya mutu nan take, mahaifinmu ya wanzu. Don haka sai mahaifinsa ya sanya masa suna Falilu, watau wanzajje. Mahaifinsa ya rene shi har zuwa girmansa, ya yi masa aure da mahaifiyarmu, sa'annan ya kwanta ya mutu. Yayin da mahaifiyarmu ta sami ciki sai ta haifi wannan dan uwan nawa na farko, aka sanya masa suna Mansur. Ta sake samun ciki, ta haifi wannan dan uwan nawa na biyu, mahaifinmu ya rada masa suna Nasiru. Da ta sake samun ciki na uku sai aka haife ni, mahaifina ya sanya mini suna Abdullahi. Mahaifinmu ya rene mu tare cikin tsananin kulawa har sai da muka isa munzalin mutane, sai ya kwanta ciwon ajali ya mutu. Ya bar mana gadon gida da rumfarsa ta kasuwa wacce take cike da dukiya ta daga dukkan tufafin Hindu,da na Rum, da na Hurassana, da wadansun wadannan, tare da tsabar kudi har dinari dubu sittin. Muka wanke gawar mahaifinmu, muka yi masa jana'iza, muka kai shi masaukinsa na karshe, muka gina kubba mai girma a wurin domin girmamawa gare shi. Muka gayyaci malamai wurin kabarinsa, suka yi ta sauke Kur'ani mai girma tsawon kwanaki arba'in domin nema masa gafara, da nema masa tsari daga shiga wuta. Bayan an yi sadakar arba'in sai na gayyaci dukkan tajirai da manyan gari na shirya musu walima, aka ci aka sha aka tumbatsa. Da aka gama cin abinci sai na mike na ce musu, "Ya ku mutane, ku sani cewa wannan duniya ba matabbata ba ce, lahira ita ce gidan dawwama. Girma da daukaka sun tabbata ga wannan wanda ba ya gushewa har abada. Shin ko kun san dalilin da sa ya sa na kira ku nan, a cikin wannan rana mai albarka?" Suka amsa mini, "Allah shi ne masani a dukkan abin da yake boye." Na ce musu, "Mahaifina ya mutu ya bar kudi masu yawa, to ban sani ba ko akwai wanda ke bin sa bashi daga cikinku. Idan akwai mai bin sa bashi sai ya yi magana ya ce, 'ina bin sa abu kaza da kaza' ni kuwa in biya shi saboda in sauke masa nauyin da ke kansa wanda bai sami saukewa ba." Dukkansu suka amsa mini, "Ya Abdullahi, hakika duniya gidan rudi ce, lahira ita ce gidan tabbata. Wane kinibibi zai sa mu ce muna bin mahaifinka bashi, don dai son abin duniya. Dukkanmu mun san cewa cin dukiyar marayu babban laifi ne. Allah ya ji kan mahaifinka da rahama, ba mu san mai bin sa bashi ba, shi ne ma ke biyar mutane da yawa. Mahaifinka ba abin da ya ke gudu irin cin bashi, sau da yawa mukan ji shi yana addu'a, 'Allah ka tsare da cin bashi, Allah ka da ka dauki raina da bashin mutane ga wuyana.' Dukkanmu shaidu ne, idan ya dauki bashin mutum, nan da nan yake biyansa ba tare da mai kayan ya matsa masa ba. Idan kuwa kayansa aka dauka bashi, to ba ya takura wa wanda ya amshi kayan, idan ma talaka ne sosai sai ya yafe masa. Idan kuma ba talaka ba ne kuma mutumin ya mutu bai biya shi ba sai ya ce, 'na yafe masa,
No comments:
Write Comments