Wednesday

Home › › Munyi dãna sanin kai hari kan farar Hula |→ Nigerian Soldiers
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana damuwarta kan wani harin bam da sojojinta suka kai wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kauyen Raan a karamar hukumar Kale-Balge da ke jihar Borno.Mai magana da yawun rundunar sojin Janar Rabe Abubakar, ya ce sun sami labarin cewa akwai mayakan Boko Haram ne a kauyen na Raan shi ne aka yi niyyar kai musu hari.
Amma bayan da sojoji suka gane harin ya fada kan farar hula ne 'sai muka shiga cikin dimuwa kan abin da ya faru,'' in ji shi.
Fiye da mutum 50 ne suka mutu a harin yayin da wasu kusan 200 suka jikkata, a cewar kungiyoyin agaji.
Janar Rabe ya ce duk da cewa a kan samu irin wannan kuskure lokaci zuwa lokaci a yankunan da ake yaki, amma ''al'amarin ya kada mu matuka kuma muna cikin da-na-sani sosai."
Wani kwamanda a rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor ya ce za a yi bincike kan yadda aka yi wannan 'kuskure', domin a guji maimaita irinsa a gaba..
Shi ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta kan lamarin ya kuma yi alkawrin taimaka wa jihar Borno ta duk irin yadda ya dace.
'Hukumomin agaji'
Kakakin kungiyar MSF Etienne l'Hermitte ya yi kira ga mahukuntan Najeriya da su taimaka wajen kwashe mutanen da suka samu raunuka ta sama da ta kasa.
"Jami'an kiwon lafiyarmu a kasashen Kamaru da Chadi a shirye suke su duba wadanda suka jikkata", in ji shi.
MSF ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su mutanen da suka gudu daga matsugunansu ne a yankunan da 'yan Boko Haram ke kai hare-hare.
Rahotanni sun ce lamarin dai ya rutsa da jami'an tsaro da dama, inda wasu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu raunuka.
Rundunar sojin ta ce tana amfani da jirage masu saukar ungulu domin kwashe wadanda suka jikkata.
Hukumomin agajin sun kasance suna shiga yankunan da ake fama da rikicin domin taimakawa da abinci da magunguna da sauran kayan bukatun yau da kullum.
A watan da ya gabata ma Majalisar Dinikin Duniya ta bukaci a hada dala bilyan daya domin a tallafawa masu fama da yunwa a yankin.
Ta ce fiye da mutane miliyan biyar ne ake sa ran za su fuskanci matukar yunwa sakamakon rashin amfanin gona da aka yi shekara uku a jere ba a samu ba a yankin.
A yanzu haka mutum 100,000 ne suke bukatar taimakon gaggawa musamman kananan yara da suke fama da matsananciyar yunwa.
Waiwaye kan Boko Haram:
Kungiyar Boko Haram ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya da makwabtan kasashe irinsu Kamaru da Chadi da Nijar.
Kungiyar na yakar gwamnati ne da kuma da'awar jihadi domin shimfida daular musulunci.
Sai dai tun a shekarar da ta gabata gwamnatin Najeriya ta fara karya lagon mayakan har kungiyar ta rage karfi.
Amma a makonnin da suka gabata sun kara karfafa kai hare-hare saboda zuwan yanayin rani ya sa sun samu sararin samun maboya a surkukuin daji sosai.

 • A shekarar 2002 ne Boko Haram ta far samuwa da kuma bayyana akidunta na kin karatun Boko.

  A 2009 kuma ta fara kai hare-harenta yawanci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

  Inda ta kashe mutane da dama, ta raba miliyoyi da muhallansu.

  Kungiyar ta kuma dinga sace tare da yin garkuwa da mutane.

  A shekarar 2015 ne Boko Haram ta sanar da yin muba'ya'arta ga kungiyar IS.
 • No comments:
  Write Comments