Sunday

Home › › Shugaba Buhari Na Cikin Koshin Lafiya | Femi Adesina
Yayin da shugaba Mohammadu Buhari ke
kasar Ingila domin yin hutu da kuma duba
lafiyarsa, sai gashi kuma ya bar baya da
kura.Yanzu haka a
Najeriya ana ta cece-kuce game da
halin kiwon lafiyarsa da ma rayuwarsa
baki ‘daya, tun lokacin da ya tafi Ingila
hutun shekara-shekara da ya saba.


A wata sanarwa da Femi Adesina, mai
baiwa shugaban Najeriya shawara akan
harkokin yada labarai, yayi tur da
Allah wa dai da wasu ‘yan Najeriya
musamman ‘yan adawa dake amfani da
wannan ziyara da duba kiwon lafiyar
shugaban kasa a matsayin abin cece-
kuce, na cewa yana cikin tsananin
rashin lafiya ko ma ya rasu.
Yace gwamnati na nan akan bayanin
da ta bayar tun farko cewa shugaba
Buhari yana hutu ne kuma zai yi
amfani da lokacin hutunsa domin
likitoci su duba lafiyarsa.
Alhaji Umaru Dembo, ‘daya daga cikin
iyayen jam’iyyar APC a Najeriya, ya
nuna damuwar kan ra’ayoyin da ke
fitowa daga gurin ‘yan Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan
Umar Faruk Musa.
No comments:
Write Comments