VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Tuesday

Home › › Sojojin Nigeria sun Kashe fararen hula '50' ∅
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta hallaka tare da jikkata fararen hula bisa kuskure a kauyen Rann, da ke Kala Balge a jihar Borno.
Kungiyar likitocin sa kai ta MSF ta ce mutane akalla 50 ne suka mutu, yayin da 100 suka jikkata.
Ma'aikatan agaji na cikin wadanda suka samu raunuka - kungiyar bada agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar shida daga cikin ma'aikatanta.


Harin ya faru ne a kauyen Rann da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, inda sojoji ke fafatawa da mayakan Boko Haram.

Wani kwamanda a rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor ya ce matukin jirgin yakin ya kai hari kan mutanen ne a bisa kuskuren cewa 'yan Boko Haram ne.

Ya ce an bashi umarni ne a bisa bayanan sirri game da wuraren taruwar mayakan Boko Haram.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon nuna takaici da kuma jaje, game da asarar rayukan da aka yi, ya kuma yi kira da a kwantar da hankali.

Kakakin fadar shugaban kasar, ya ce gwamnati za ta tallafawa gwamnatin jihar Borno game da wannan abin bakin ciki da ya faru.

Kakakin kungiyar MSF Etienne l'Hermitte ya yi kira ga mahukuntan Najeriya da su taimaka wajen kwashe mutanen da suka samu raunuka ta sama da ta kasa.

"Jami'an kiwon lafiyarmu a kasashen Kamaru da Chadi a shirye suke su duba wadanda suka jikkata", in ji shi.
MSF ta ce akasarin wadanda harin ya rutsa da su mutanen da suka gudu daga matsugunansu ne a yankunan da 'yan Boko Haram ke kai hare-hare.
Rahotanni sun ce lamarin dai ya rutsa da jami'an tsaro da dama, inda wasu suka mutu yayin da wasu kuma suka samu raunuka.

Rundunar sojin ta ce tana amfani da jirage masu saukar ungulu domin kwashe wadanda suka jikkata.
No comments:
Write Comments