Friday

Home 2019 Ba za'a yi Zabe ba : A cewar femi fani kayode


femi fani kayode.


Wani tsohon Minista kuma babban Dan
adawar shugaban kasar Najeriya
Muhammadu Buhari, Femi Fani-Kayode
yace ba za a gudanar da zabe ba a kasar
nan a shekarar 2019.


Ko dai me zai hana a gudanar da zaben
shekarar 2019, sai ace Oho. Cif Femi
Fani-Kayode wani tsohon Ministan
sufurin jirgin sama da kuma al’adu duk
a lokacin shugaba Olusegun Obasanjo
yayi wannan ikirari kwanan nan.


Femi Fani-Kayode wanda rikakken dan
PDP ne, na kuma hannun daman tsohon
shugaba Jonathan Goodluck dai yace
Gwamnatin shugaba Buhari ta kawo
bala’i da masifa cikin kasar. FFK yace
dole ayi ta addu’a sannan a cirewa
Gwamnatin iskokan da ke damun ta.


muhd buhari


Fani-Kayode dai rikakken dan adawar
shugaba Buhari ne kamar yadda kowa
ya sani, ya bayyana wannan ne a
shafin san a Twitter mai lamba
@realffk. Kwanan yake ba’a ga lafiyar
shugaban kasar yake cewa ba ya iya
wuce watanni 20 yana mulki kamar dai
yadda aka kare a wancan lokacin na
Soji.
Mukaddashin shugaban kasa Farfesa
Yemi Osinbajo kuma ya shirya farfado
da tattalin arzikin Najeriya cikin
watanni biyu. Najeriyar dai ta samu
durkushewar tattalin arziki a a bara.

hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments