Wednesday

Home › › A jihar Bauchi matasa sunyi gangamin goyon bayan shugaba buhari
A yau Laraba ne dandazon matasa suka fito kan tituna a cikin garin Bauchi inda suke nuna goyon bayansu da kuma kara bayyana soyyarsu ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, kana sun yi masa addu’ar samun sauki daga jinyar da ya je yi. Wakazalika sun bayyana wa al’umma cewar Buharin na nan cikin koshin lafiya.

Gangamin wacce ta taso daga kofar Stadium kana ta shiga cikin garin na Bauchi inda suka zagaya manya da kananan titinan jihar.

Nasiru Gwallaga shugaban matasan jam’iyyar APC ne ya jagoranci gangamin inda ya shaida wa LEADERSHIP Hausa cewar “Makasudin wannan fitowar namu shi ne domin nuna goyon bayanmu ga gwamnatin APC da kuma kara nuna soyyaryarmu ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a bisa kokarin da ya ke yi wajen ciyar da kasar nan gaba, sannan mun yi amfani da wannan damar wajen nuna soyyarmu ga Gwamnan Bauchi da ba shi goyon baya a bisa kokari da ke yi wa jahar nan ta Bauchi”.

In ji Sa
Nasiru shugaban A-Kasa-A-Tsare ya ci gaba da bayyana cewar sun yi amfani da wannan tunanin ne domin zai taimaka wa shuwagabanin wajen kara himma da kwazo wajen yin aiyukan ya yake kansu kana su samu sauke alkawuran da suka yi wa talawansu.


@facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments