VISIT US ON AREWASOUND.COM


HOTTREND ONLINE :
Music Mp3 - Sabuwar Wakar Hamisu Breaker mai suna - Bazana Manta Maryam Ba.
CHECK NEW PRODUCTS HERE
Hamisu breaker 2020 Album Download Mp3 music

Sammani aa 2020 Album : Download Complete Album (Akwai lokaci)

Umar M Shareef Zeenaru 2020 Official AUDIO+VIDEO

MUSIC: Melery 2020 Song Da Dadi So

Tuesday

Home › › Abin Da muka Tattauna Da buhari yayin da muka yi waya | OSINBAJO
Mukaddashin shugaban kasa Yemi
Osinbajo ya kara tabbatar da cewa
Muhammadu Buhari na nan cikin
koshin lafiya. Osinbajo yace kuma
Buhari zai dawo Najeriya yana
kammala gwajin da yake yi a asibiti.


Osinbaji yayi doguwar waya da
Muhammadu Buhari ya kuma
bayyanawa ‘Yan Jaridan da ke Fadar
shugaban kasar abin da suka tattauna a
wayar. Osinbajo yace sun tattauna ne
game da tattalin arzikin kasa da kuma
batun kasafi da Buhari.

Mukaddashin shugaban kasa Osinbajo
yace ya kuma fadawa Buhari cewa ana
zanga-zanga a kasar inda mutane ke
kuka musamman game da tattalin
arziki. Sannan kuma dai Osinbajo yayi
watsi da rade-radin cewa ana nema a
tursasa ya sauka daga kan kujera, yace
babu wanda ya isa.

A jiya ne aka gudanar zanga-zanga ga
Gwamnatin Buhari saboda halin da ake
ciki a Kasar a halin yanzu. Wani
Babban Jigo Jam’iyyar APC mai mulki
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kira
ga ‘Yan Najeriyan da su kara hakuri.

@fb.com/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments