Saturday

Home › › An dakatar da bin umarnin dokar donal trump a kan musulmi
 • An yi zanga-zangar adawa da manufofin Trump a kasashen duniya • Hukumomin Amurka sun dakatar da bin umurnin dokar da Donald Trump ya kafa ta haramtawa wasu ‘yan kasashen musulmi bakwai shiga kasar, bayan wani alkalin kotu ya soke dokar a yau Asabar.
  Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da hukuncin na kotun kasar da ta dakatar da matakinsa na haramtawa wasu kasashe bakwai na musulmi shiga Amurka.

  Trump ya rubuta a shafin shi na Twitter cewa zai kalubalanci hukuncin wanda alkalin wata kotun Amurka James Robert ya zartar.

  Tuni dai kamfanonin jiragen sama suka sanar da komawa aikin jigilar fasinja a kasashen da Trump ya hana shiga Amurka a makon da ya gabata.
  Alkalin kotun ya ce umurnin da Trump ya sanyawa hannu ya saba dokar kasa.

  Amma a martanin da ya mayar, shugaba Trump ya ce duk kasar da ba ta iya tantance wanda zai shigo ya fita domin tsaron kasa, matsala ce babba.
  Kasashen da haramcin na Trump ya shafa sun hada da Iran da Iraq da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen.

  kasance DA mu @fb.com/hausapost28
  No comments:
  Write Comments