Monday

Home › › An gãno maboyar boko haram A jihar kano
Hukumar yan sanda sun gani wata
mabuyar Boko Haram a jihar Kano.
Hukumar yan sandan ta gano hakan ne
a wata farmaki da ta kai tare da
hukumar tsaron farin hula wato
Nigerian Securities and Civil Defence
Corps, da hukumar Hizbah da kuma yan
banga a jihar.


Jaridar New Telegraph ta bada rahoton
cewa hukumomin tabbatar da tsaro sun
farka daga bacci ne bayan wata farga
da gwamnan jihar Dakta Abdullahi
Ganduja yayi akan cewa yan Boko
Haram sun shigo jihar Kano.
Rahoton tace hukumomin tsaron na
dube-dubentane inda ta gano mabuyar
kuma an damke yan Boko Haram 53
bisa ga rahoton ta aka samu.

Yayinda suke tabbatar da kamun,
kakakin hukumar yan sanda a jihar,
DSP Magaji Musa Majiya, yace yan Boko
Haram 53 da aka kama kari ne akan
mutane 840 da aka damke a fadin
tarayya.

Rahoton ya kare da cewa ana gudanar
da bincike akan yan Boko Haram din.

fadi ra'ayin ka @ HAUSAPOST28/RA'AYOYI
No comments:
Write Comments