Thursday

Home An gano wani kauye a Turkiyya wanda idan aka shaki iskarsa ake warke wa daga ciwon Kansa
An gano wani kauye a Turkiyya da in aka shaki iskarsa ake warke wa daga ciwon Kansa
• • • •
Kauyen Ayvacık da ke tsaunin Spil a lardin Manisa na kasar Turkiyya ya daukaka wajen maganin ciwon daji.


Jama'a daga kowanne sassa na duniya na tururuwa zuwa kauyen don neman waraka.
Sarakunan Daular usmaniyya na zuwa kauyen a lokacin da ba su da lafiya kuma daga lokacin da aka san shi a kasashen waje sai jam'a daga kasashen duniya da suka hada da Ingila, Holan, Faransa, Amurka da Jamus suka dinga dunduma zuwa kauyen da ke kan tsauni.

Tsaunin na Spil na da tudun mita dubu 1522. Kuma a yanzu ana kiran kauyen da "Likitan kauye" Kuma malami Nursel Karaosmanoğlu Şimşek ya ce, ya je kauyen kuma ya samu waraka daga ciwon dajin huhu.

Tun bayan jin hikayar Şimşek ne jama'a suka fara tururuwa zuwa Ayvacık din don neman waraka.


Kuma akwai wani da ya ke zama a Istanbul yana da ciwon daji na a cikin jini da ya ziyarci kauyen na wasu 'yan kwanaki, bayan ya koma Istanbl sai likitoci suka yi mamakin yadda ya samu lafiya.

HOTUNA

No comments:
Write Comments