Wednesday

Home › › An haifi wani jariri mai kai biyu a kasar Indiya (Hotuna) -.
Jaririn da aka haifa mai kai biyu
ya riga mu gidan gaskiya


Wata mata mai shekaru 30 ta haifi wani
jariri mai ban al’ajabi a kasar Indiya, shi
dai wannan jaririn halittarsa tazo ne da kai
guda biyu.

.


Sai dai kash! Jaririn ya rasu awanni
kalilan bayan haihuwarsa.
Mahaifiyar jaririn ta haife shi ne ta
hanyar tiyata, wanda aka yi a babban
asibitin SP dake kasar Indiya, kuma ta
bayyana ma likitoci bata da masaniyar
yanayin halittar jaririn.

Yayin da take yi ma yan jarida bayani,
mahaifiyar tare da mahaifin yaron sun
shaida ma manema labarai cewa sai a
jajibarin tiyatan ne suka samu labarin
yanayin halittar jaririn nasu, kamar
yadda wata jarida ta ruwaito.
Iyayen yaron, Muhammad da Nasreen
sun fahimci halittar yaron nasu ne
bayan daukan hoto da aka yi ma cikin
matar, sai dai iyayen sun ce ba zasu
taba kyamar yaron nasu ba duk da irin
halittar daya zo da shi.
Bayan haihuwar jaririn, sai likitoci
suka bayyana yaron a matsayin dan
baiwa, inda iyayen yaron suka ce
wannan baiwa ne daga Allah.

Likitoci sun bayyana cewar yiwuwar samun
jariri mai kai biyu daya ne cikin
haihuwa 100, 000.

Kamar yadda masana suka ce, ana
samun jariri mai biyu ne idan kwan
dake cikin mahaifar mace basu rabu da
juna ba bayan saduwa da maniyyi.

“sai dai yawancin jarirai masu irin
wannan halittan suna mutuwa ne
saboda gabobinsu basa iya daukan
dawainiyar su.”
inji masana.

Kashi 40 na jariran da ake haifa a hade
suna mutuwa ne kafin a haife su, yayin
da kashi 35 kuwa suna mutuwa ne
bayan haihuwarsu.
Ga wani bidiyon jarirai da aka haifa a
hade:

hausapost28 on Facebook
No comments:
Write Comments