Tuesday

Home › › An kai Harin kunar bakin wake a wata kotun Koli......
Mutane kusan 20 suka mutu a harin kunar bakin wake da aka kai a kotun Koli a Kabul

kasance damu @facebook/hausapost28

Wani dan kunar bakin wake ya kashe mutane 19 bayan ya tayar da bom a kotun Kolin Afghanistan da ke Kabul a yau Talata. Harin ya kuma raunana mutane 41.

Cikin wadanda suka jikkata sun hada da mata da yara.
Ministan cikin gidan kasar ya ce, maharin ya tayar da bama-baman da ke jikinsa ne a harabar ajiye motoci, a dai dai lokacin da ma’aikata ke shiga mota bayan sun tashi daga aiki.
Ko a watan jiya, sai da kungiyar Taliban ta kai makamancin wannan harin a wani ofishin majaliasar wakilan kasar, inda ta kashe mutane 30 tare da jikkata 80.
Afghanistan dai na ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga mayakan Taliban da al Qaeda da kuma IS bayan ficewar sojojin kungiyar tsaro ta NATO a kasar.

No comments:
Write Comments