Wednesday

Home › › An kashe 'yan tawayen Shi'ar Houthi 19.

Mayaka 'yan tawayen Shi'ar Houthi 19 aka kashe sakamakon harin da kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kai a lardin Hajja da ke arewa maso-yammacin kasar Yaman.An kashe 'yan tawayen Shi'ar Houthi 19 a Yaman.


Mayaka 'yan tawayen Shi'ar Houthi 19 aka kashe sakamakon harin da kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kai a lardin Hajja da ke arewa maso-yammacin kasar Yaman.

Sanarwar da aka fitar ta shafin facebook mallakar kawancen kasashen na Larabawa an bayana cewa, jiragen saman kasashen da Saudiyya ke jagoranta sun kai hari a gundumar Harad ta lardin Hajja inda aka kashe kwamandan Houthi Ahmad Hassan Al-Jarb.

A rikicin da aka fafata da 'yan Shi'ar da sojin gwamnatin Yaman a gundumar Midi kuma an kashe 'yan Shi'ar Houthi 18, amma sanarwar ba ta bayyana ko an kashe wani jami'in soji ko jikkata wa daga rundunar sojin Yaman.

A rubutacciyar sanarwar da Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan aiyukan Jin Kai a kasar Yaman Jamie McGoldrick ya ce, akwai mutane miliyan 7 da yunwa ke barazanar kashe wa kuma akwai wasu miliyan 17 da ba sa samun isasshen abinci.
Mc Goldrickya kuma ce, ana ci gaba da samun rikici a kasar ta Yaman.hausapost28 on facebook
No comments:
Write Comments