Saturday

Home An samu nasaran yin aikin fidar zuciya a asibitin Aminu Kano.Mataimakin darektan yada labarai na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Aminu Inuwa ya ce asibitin ta sami nasaran yin fidar zuciya ma wani mara lafiya mai suna Shehu Bashir-Nababa.
Ya fadi hakan ne wa manema labarai ranar Juma’a a jihar Kano.


Ya ce an kawo majinyacin wato Bashir-Nababa asibitin saboda raunin da aka gano ya na dauke dashi a zuciyasa ta dalilin hadarin mota da yayi.
Aminu ya ce aikin fidar ya dauke su tsawon awa daya da rabi a dakin fida.

Inuwa ya yi bayanin yadda likitocin suka yi fidar cewa zuciyar majinyacin ta toshe ne saboda zuciyar bata bugawa yadda ya kamata saboda haka ya sa dole sai anyi wa majinyacin aiki domin zuciyar ta sa ta fara aiki yadda ya kamata.

Likitan daya shugabanci likitocin da suka yi fidar ya yi kira ga mutane da su yi kokarin zuwa asibiti da zaran sunji ba daidai ba ajikinsu musamman abun da ya shafi bugawar zuciyarsu.
Awowi 48 bayan majinyacin ya farfado ya godewa wa Allah sannan ya godewa likitocin da suka yi aikin akansa.
No comments:
Write Comments