Friday

Home › › An Yi Kira ga Majalissar Kasa da ta tabbatar da magu | EFCC
Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Taraba, Alhaji Isa Tafida Mufindi ya yi kira ga Majalisar Dattawan kasar nan da ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar EFCC, kamar dai yadda Shugaban kasa ya sake gabatar mata sa sunansa. Mafindi ya yi wannan kira ne a wata zantawa da ya yi manema labarai a kwankin baya. Dan siyasar ya ce yana wannan kira ne bisa la’akari da irin gudumawar da Magun ke bayarwa wajen yakin da cin hanci da rashawa a kasar nan, wanda hakan zai taimaka wa kudurin Shugaba Muhammadu Buhari a wannan yaki da yake yi. Ya ce, tabbatar da shi kan wannan mukami zai kara masa azama kan abin da yake yi yanzu.

Ya ci gaba da cewa muddin ana so Shugaba Muhamamdu Buhari ya samu cika alkawarinsa da ya yi lokacin yakin neman zabe na ganin bayan cin hanci da rashawa a kasar nan, to lallai akwai bukatar da a tabatar da Ibrahim Magu bisa wannan mukami. Alhaji Mafindi ya ci gaba da cewa, kwarewa a harkar yaki da cin hanci da rashawa irin na Ibrahim Magu zai matukar taimaka wa Shugaban kasa, wanda kuma bai kamata a ce ana samun wannan jinkiri wajen tabbatarda shi din ba.
©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments