Thursday

Home › › An yiwa shekau barazanar shiga wutar jahannama direct
kanin marigayi Farfesa Aliyu Usman Mani
ta Jami'ar Maiduguri ya lahananci
shugaban 'yan boko Haram Abubakar
Shekau a wata budaddiyar wasika.


Malam Usman Abbas, kane marigayi
Farfesa Aliyu Usman Mani, wanda aka
kashe a lokacin wani harin kunar bakin
wake a Jami'ar Maiduguri (UNIMAID),
ya ce Abubakar Shekau matacce ne a
raye wanda makomarsa wutar
Jahannama.

Usman ya bayyana wannan a cikin
wani budeden wasika ga Abubakar
Shekau, shugaban Boko Haram a wata
bangare. Jaridar News gency ta Najeriya
(NAN) ta rahoto wannan labari ranar
Alhamis a Maiduguri babban birnin
jihar Borno.
Na saurari sautin sakon ka inda ka ce
ka dauki alhakin harin kunar bakin
wake da ya kashe dan'uwana Farfesa
Aliyu Usman Mani da wayansu a
lokacin sallah asuba a masallacin
ma’aikatar Jami'ar Maiduguri babban
birnin jihar borno a ranar Litinin 16 ga
watan Janairu, 2017.

Jawabi na a wannan wasika zuwa gare
ka shine wuta jahannama ne makoma
duk wanda ke hallaka rayuwar
al’umma.
Sabanin da'awar ka a cikin mafi yawan
bidiyo da kuma sautin sakonnin ba
gaskiya ba ne, mutane marar laifi da ka
hallaka sun fika daraja a idanun jama’a
da kuma Allah. Rayuwar ka ba za ta
samu alfarmar Allah ba.
Asara na kawai ita ne hawayen da na
zubar a kan rasuwar marigayin. Amma
duk da haka, ina matuƙar farin ciki
domin ya kare ne a cikin masallaci a
inda ya ke bautawa Allah kuma ya
kazance da azumi a ranar Litinin da
aka kai harin.
Akika munji zafin mutuwarsa, amma
ina so in gaya muka cewa ba za ka iya
dakatar da mu daga zuwa masallaci
domin yin ibada kuma ba za ka iya
hana mu daga neman ilmi addini da
kuma na zamani.


kasance damu @ @fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments