Tuesday

Home › › APC Ta Nada Kwamitin dai-daita Suhun ‘Yan Jam’iyyar.APC Ta Nada Kwamitin Suhunta ‘Yan Jam’iyyar

Shugabannin jam’iyyar APC sun nada sabon kwamiti domin shirya wadansu ‘ya’yan jam’iyyar da ba sa ga maciji a tsakaninsu. Jam’iyyar ta ce ta yi hakanne domin hada kan ‘ya’yan jamiyyyar a jihohin da ake da matsaloli tsakanin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar. Ana dai samun irin wadannan matsalolin akalla jihohi 12 da jam’iyyar ke fama da su.

Wasu daga cikin rikicin da jam’iyyar ke fama da su sun hada da: Rikicin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani da kuma jihar Kano tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wadanda suka fi muni a cikin su.


Kakakin Jam’iyyar APC Bolaji Abdullahi, ya ce, jam’iyyar ta na so ta ga cewa ta dinke duk wata baraka ce da take neman hadiye’ya’yan jam’iyyar a ko’ina a fadin kasar nan ganin cewa za’a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Afurilun wannan shekaran. Wasu jihohin da ke fama da wannan matsalar sun hada: Nasarawa, Bauchi, Bayelsa, Zamfara, Kogi, Adamawa da sauransu.


like us on Facebook
No comments:
Write Comments