Friday

Home › › Bankin duniya ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa.
world bankA kwanakin baya ne bankin duniya ya fitar da wani rahoto game da bunkasuwar biranen kasashen Afirka, inda ya kalubalanci kasashen Afirka da su kara zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa da yin kwaskwarima kan kasuwar yankunan kasa don gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin biranen kasashen. Rahoton bankin wanda aka fitar a kasar Habasha ya bayyana cewa, zuba jari a fannin gina kayayyakin more rayuwa da yin kwaskwarima kan kasuwar yankuna su ne batutuwa masu muhimmanci yayin da ake kokarin gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da kara samar da ayyukan yi da kara karfin biranen kasashen Afirka. Muddin kasashen Afirka suna bukatar tattalin arzikinsu ya bunkasa, tilas ne biranen kasashen Afirka su bude kofofinsu ga sauran kasashen duniya.


Rahoton ya kuma bada shawara cewa, kamata ya yi kasashen Afirka su daidaita bunkasuwar ayyukan more rayuwa, gidaje, masana'antu, ciniki yayin da suke kokarin raya biranensu, da kara bullo da ka'idojin da suka shafi harkokin kasuwannin yankuna, da tabbatar da 'yancin mallakar yankunan, da kuma tsara shirin raya birane da suka dace.
®facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments