Saturday

Home › › Bikin kaddamar da shugaban Gambiya

Shugaba Adama Barrow na Gambiya zai yi bikin kaddamar da kansa tare da bikin tunawa da samun 'yancin kasar daga Birtaniya.
A wannan Asabar ake kaddamar da Shugaba Adama Barrow na Gambiya kusan wata guda bayan da ya dauki madafun iko, bayan nasara kan tsohon Shugaba Yahya Jammeh. Shi dai Shugaban ya dauki madafun iko a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Dakar na kasar Senegal, saboda yadda lokacin Shugaba Jammeh ya ki mika wuya, kafin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta tursasa masa ficewa daga kasar zuwan Equatorial Guinea.
Bikin na wannan Asabar da za a yi a gaban manyan baki da sauran dubban mutane domin kaddamar da Shugaba Adama Barrow ya zo dai-dai da lokacin da kasar ta Gambiya da ke yankin yammacin Afirka take bikin cika shekaru 52 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a shekarar 1965.

HAUSAPOST28 on Facebook click and like
No comments:
Write Comments