Tuesday

Home Buhari mutum mai gaskiya da kishin kasa – Inji Shagari
Buhari/shagari.


Tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya yabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ke kokarin ganin ya gyara kasa Najeriya.
Shagari ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya, rikon amana da kishin kasa.Yace kokarin da Buhari yakeyi musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa sannan da seta Najeriya akan tafarkin kwarai abu ne wanda ya cancanci yabo.

Shagari ya kara da cewa dole a jinjina ma Buhari akan yadda ya ke ta kokarin ganin ya farfado da tattalin arzikin kasa Najeriya da irin shirye shirye da gwamnatinsa ta bullo dasu domin samun nasara akan hakan.

Shagari ya fadi hakanne a yayin da yake jawabin murnan zagayowar ranar haihuwarsa a garin Sokoto.

Shagari ya shekara 92 a duniya.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana kasan Ingila inda ya ke hutu da duba lafiyarsa.
Ya kira sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman jiya domin mika ta’aziyyar sa ga sarkin a dalilin rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Aminatu Mai Babban daki.
No comments:
Write Comments