Monday

Home Buhari Na Kan Hanya : Obasanjo

Buhari bai gaza ba -Obasanjo


Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun
Obasanjo yace ko da wasa shugaba
Muhammadu Buhari bai gaza ba wajen
tafiyar da mulkin kasar tun karbar
ragamar tafiyar da mulki a shekarar 2015.
A wata hira da yayi da kamfanin
dillancin labaran Najeriya, Obasanjo
yace Buhari yayi iya bakin kokarin sa,
kuma ko kadan bai damu da korafin da
yake ji wasu na yi kan shugabancin ba.

Tsohon shugaban ya yaba kan matakan
da ake dauka wajen yaki da cin hanci
da rashawa dan kwato dukiyoyin
jama’a da kuma yaki da ta’addanci a
karkashin gwamnatin Buhari.

Obasanjo ya ce a baya ya koka kan
yadda Buhari ke tafiyar da harkokin
diflomasiya amma yanzu ya ga an samu
sauyi, yayin da ya bayyana ci gaba da
goyan bayan shugaban da kuma fatar sa
na ci gaba da ganin Najeriya ta kasance
kasa guda.
No comments:
Write Comments