Sunday

Home › › Buhari ya kara tsawon hutun sa a London
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara tsawaita lokacin hutunsa kamar yadda ya sanar da majalisa don ci gaba da samun magani a London a yayin da 'Yan Najeriya ke dakun isowarsa Abuja.

Femi Adeshina mai magana da yawun shugaban ya fadi a cikin wata sanarwa cewa, shugaban ya sanar da Majalisa a rubuce a yau Lahadi kan bukatar tsawaita lokacin hutunsa domin samun damar kammala gwaje gwajen lafiyarsa da karbar sakamako.

A yau ne dai shugaban ya kamata ya dawo Abuja fadar gwamnatin Najeriya, Amma Sanarwar ta ce likitocin Buhari ne suka bukaci ya tsawaita hutun.
Sanarwar kuma ta ce shugaban ya mika godiyarsa ga ‘Yan Najeriya da ke masa addu’o’i da fatan alheri.


kasance damu @fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments