Thursday

Home › › Daesh na cikin halin tsaka mai wuya a garin Al-Bab
image


Kwamandan da ke jagorantar kasashen duniya dan kasar Amurka don kai hare-hare kan 'yan ta'addar Daesh Kanal John Dorrian ya bayyana cewa, 'yan ta'addar na cikin halin tsaka mai wuya a garin Al-Bab na kasar Siriya.


Turkiyya da sojojin da ta ke marawa baya suna gagarumin aiki a Al-Bab.

Dorrian ya kuma ce, kungiyar na cikin mawuacin hali kuma tana bukatar 'yan ta'adda da dama kafin ta iya rike iko da garin na Al-Bab.

Dorrian ya tattauna ta hoton bidiyo da ma'a,katar tsaro ta Amurka Prntagon inda ya bayar da bayanai game da hare-haren da ake kai wa a Siriya da Iraki.
Kanal Dorrian ya kuma ce, Sojojin Turkiyya da kuma wadanda Turkiyya ke mara wa baya sun shiga garin Al-Baba ta bangaren arewa su kuma kawancen kasashen duniya na kai hari ta sama, dakarun gwamnatin Siriya kuma suna matsa wa ta bangaren kudu wanda hakan ya jefa Daesh cikin halin tsaka mai wuya.


@facebook/hausapost28

No comments:
Write Comments