Wednesday

Home › › Dakarun Turkiyya sun Shiga Tsakiyar Garin Al-Bab
Kakakin shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya bayyana cewa, dakarun kasarsu sun shiga tsakiyar garin Al-Bab domin fatattakar 'yan ta'addar Daesh.
Ibrahim Kalın ya amsa tambayoyin 'yan jaridu a yayin wata tattauna wa da kafar yada labarai mai zaman kanta.


Da aka yi masa wata tambaya game da hare-haren da Turkiyya ke kai wa don Tsaron Yankin Fırat a arewacin Siriya sai ya ce, "Sun shiga tsakiyar garin Al-Bab. Kuma muna magana da Rasha kan yadda ba za mu yi arangama da dakarun Assad ba."

Kalın ya kuma ce, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana tattauna ta wayar da tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump.

Kalın ya ce, tattaunawarsu da Rasha ta yi amfani tare da samar da sakamako mai kyau inda nan da wani lokaci shugabannnin kasashensu 2 za su gana.

Ya ce, a tattaunawar an tabo batun kasar Siriya, inda Trump ya kuma nuna amnince wa game da bukatar kafa yankin zaman lafiya mai girman kilomita dub 2 a Siriya wanda shugaba Erdoğan ya gabatar.

Kalın ya ci gaba da cewa, Trump ya tabbatar da za su sake fara tattauna batun mika wa Turkiyya shugaban 'yan ta'addar FETÖ Fethullah game da yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli.
@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments