Sunday

Home › › Dalilin Da Yasa Ba Na Sanya Kakin Kwastam | Kanal Hameed Ali

Shugaban hukumar kwastam Kanal Hameed Ali mai ritaya ya bayyana dalilin da ya sanya ba ya saka kakin hukumar da ya ke shugabanta ta kwastam tun da shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi shugabancin hukumar a shekarar 2015.


Hameed Ali ya bayyana hakan ne a gaban kwamitin harkokin kwastom na majalisar dattijai a ranar Alhamis din da ta gabata, inda ya bayyana cewa a matsayinsa na tsohon soja da ya yi ritaya a matsayin Kanal, ya sabawa al’ada ya sanya kakin wata runduna ko hukuma mai amfani da kayan sarki.

Wannan dalili na Kanal Hameed Ali ya sanya wani daga cikin mambobin kwamitin, Sanata Obinna Ogba ya fusata ya kuma ta shi ya fice daga dakin ganawar.
Sai dai kuma Sanata Dino Melaya ya kawo wa Hameed Ali misali da ko a baya ma a kasar nan a baiwa tsohon janar din soja mukamin shugaban hukumar kare hadura ta kasa FRSC wato dai Janar Halidu Hannaniya kuma ya sanya kakin hukumar ta FRSC.

Amma duk da haka Hameed Ali ya kafe akan cewa shi ba zai saka kakin hukumar kwastam ba, kuma shi ma Hannaniya da ya saka kakin FRSC ya yi kuskure.

kasance damu @fb.com/hausapost28
No comments:
Write Comments