Tuesday

Home Duk mai zuwa asibitin waje bai da kishin kasa - Ministan Buhari.Karamin ministan lafiya a Najeriya mai
suna Dr. Osagie Ehanire ya nuna matukar
rashin jin dadin sa ga yan Najeriya
musamman ma masu zuwa kasashen waje
neman lafiyar su maimakon su zauna gida
Najeriya.


Jaridar 'The Guardian' dai ta ruwaito
cewa karamin ministan yace duk mai
irin wannan halin bai da kishin kasa ko
kadan.

Karamin munistan yayi wannan
jawabin ne a garin Asaba dake jihar
Delta a ranar asabar din da ta gabata
25 ga watan Fabreru.

Nan take ne kam sai wani dan jarida ya
tambayi ministan ko ya yake ganin
maganar tasa ganin cewa yanzu haka
shugaban kasar Muhammadu Buhari na
kasar waje domin neman lafiyar sa
amma sai ya ki bayar da ansa gareshi.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa
shugaba Buhari ya tafi kasar Birtaniya
a neman lafiyar sa tun 19 ga watan
Janairu.
No comments:
Write Comments