Friday

Home › › EFCC ta kwato Naira biliyan 3 daga gidan tsohon ministan Mai
Hukumar yaki da rashawa ce ta gano kudadden a gidan tsohon ministan mai Andrew Yakubu.


Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce an samu dala miliyan 10 a gidan tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC Andrew Yakubu a wani samame da jami’an hukumar suka kai a gidansa da ke kaduna. Shugaban riko a hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ne ya shaida haka a gaban majalisar wakilan kasar yayin kare kasafin kudin hukumar na bana a majalisar.

Baya ga Dala miliyan goma an kuma kwato fam dubu saba’in da hudu na Ingila. Yakubu ya boye kudadden ne a cikin akwati mai sulke.

A makon da ya gabata dai Mista Yakubu ya shedawa hukumar cewa kwarai ya mallaki wadanan kudadden da a cewarsa kyauta ce daga wasu mutane da bai bayyana sunayensu ba.

Naira biliyan uku ne kwatankwacin kudadden da aka gano daga gidan tsohon ma’aikacin kamfanin man na NNPC. Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ce daya daga cikin muradunta sun hada da yaki DA rashawa DA kuma dakile book haram.

©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments