Tuesday

Home Ganduje ya maka wani mawaki a kotu don ya yi wa Kwankwaso wakar yabo
Gwamnatin Kano ta maka mawaki
kotu don ya yi wa Kwankwaso
wakar yaboGwamnatin jihar Kano ta maka wani
matashin mawakin Hausa mai suna Sadiq
Zazzabi a kotu ta 3 da ke jihar domin ya
bada ba'asi kan wakar da yayi wa
Kwankwaso.


Gwamnatin ta Kano ta ce tana tuhumar
mawakin ne dai bisa zargin kin mika
wakar tasa ga hukumar tantance harkokin
fina-finai ta jihar kafin ya sake ta.
Gwamnatin Kano ta maka mawaki kotu don ya
yi wa Kwankwaso wakar yabo
Shi dai Zazzabi ya saki wakar ne wadda
ya yabi tsohon gwamnan Kano Dr.
Rabi'u Musa Kwankwansao a kwanan
baya.

A kwanakin baya ne dai Shugabannin
jam’iyyar APC suka nada sabon kwamiti
domin shirya wadansu ‘ya’yan
jam’iyyar da ba sa ga maciji a
tsakaninsu.

Jam’iyyar ta ce ta yi hakanne domin
hada kan ‘ya’yan jamiyyyar a jihohin
da ake da matsaloli tsakanin jiga-jigan
‘ya’yan jam’iyyar.
Ana dai samun irin wadannan
matsalolin akalla jihohi 12 da jam’iyyar
ke fama da su.

Wasu daga cikin rikicin da jam’iyyar ke
fama da su sun hada da: Rikicin
gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai
da Sanata mai wakiltan Kaduna ta
tsakiya Shehu Sani da kuma jihar Kano
tsakanin gwamnan jihar Abdullahi
Ganduje da Sanata Rabiu Musa
Kwankwaso wadanda suka fi muni a
cikin su.
No comments:
Write Comments