Thursday

Home › › Gwamnatin cote d"Ivoire ta tattauna game da boren da wadansu sojojin kasar suka yi.

Rahotanni daga kasar Cote d'Ivoire na cewa, mahukuntan kasar sun tattauna game da boren da wasu sojoji suka yi a wani sansanin sojojin musamman dake birnin Adiaké a kudu maso gabashin kasar a ranar Talata.

image
Sojojin dai sun ci gaba da bore har zuwa safiyar ranar 8 ga wata, inda suka bazama kan tituna suna harbi cikin iska. Lamarin da ya sa aka rufe hukumomin gwamanti da makarantu da kuma shaguna a wurin.
Dangane da wannan lamarin, kakakin gwamnatin kasar ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka yi a ranar 7 ga wata cewa, fararen hula guda biyu sun jikkata a lokacin wannan bore, kuma a halin yanzu, suna samun jinya a asibitin wurin.
Ya kuma kara da cewa, gwamnati ta yi allah wadai da sojojin da suka yi wannan bore, sabo da lamarin ya bata sunan kasar gaba daya.

Bugu da kari, ya ce, ana ci gaba da shawarwari tsakanin wakilan gwamnati da na sojojin da suka yi bore, wasu wakilan sojoji za su yi shawarwari da ministan tsaro na fadar shugaban kasar kai tsaye.
A daren ranar 7 ga wata ne, wasu sojojin musamman dake sansanin suka yi harbi cikin iska, daga baya suka mamaye manyan titunan wurin, inda suka kori jama'a zuwa gida. Bayanai na nuna cewa, wadannan sojoji sun yi hakan ne don nuna rashin jin dadinsu ga matakin da gwamnati ta dauka a baya na baiwa wasu sojoji da suka tayar da bore kudi.


@facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments