Wednesday

Home › › Jami"an Tsaron Nigeria sun dakile wani harin kunar bakin wake
Rundunar 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, ta ce jami'an tsaro sun dakile yunkurin wani harin kunar bakin wake, jiya Talata a birnin Maiduguri.


Kakakin rundunar 'yan sandan Victor Isuku, ya ce wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake sun yi yunkurin kai hari da safiyar jiyan, sai dai jami'an tsaro sun cafke daya, yayin da suka harbe dayar.
Ana zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram da kokarin sake hada kansu a birnin Maiduguri, bayan sojoji sun fattake su daga dajin Sambisa da ya kasance maboyarsu a watan Disamban bara.
A yanzu dai rundunar sojin Najeriya ta kara kaimi wajen yin sintirin farautar 'yan ta da kayar bayan ta sama da kasa a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka fadada aikin nasu zuwa yankunan dake kusa da kasashen Niger da Chadi.

@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments