Wednesday

Home › › Jamus Ta kori "Yan Asalin Nigeria su dubu 12,000 zuwa mahaifarsu
Kusan ‘yan najeriya dubu 12 ne za a kora daga kasar Jamus a shekarar 2018 sakamakon yadda ba za su iya sake samun mafaka a kasar ba.

Shugaban Hukumar Kula da ‘yan Gudun Hijira ta Jamus Dr. Ralf Sanftenberg ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin waje Misi Abike Dbiri-Erewa.
Sanftenberg da ya jagoranci jami’an ofishin jakadancin Jamus da ke Abuja zuwa ofishin mai bayar da shaawarar, ya ce, ya fara aiyukan taimaka wa ‘yan najeriya ma su son koma wa gida a karan kansu.

Ya ce, suna da sama da ‘yan Najeriya dubu 37 a kasar Jamus kuma sama da dubu 12 na zaune a matsayin masu neman mafaka. Akwai yiwuwar hana su izinin zama a kasar a nan gaba wanda hakan zai sanya a takura su ta dole su koma kasarsu.

Ya kara da cewa, za a hana su izinin zama na masu neman mafalkar ne saboda Najeriya ba ta cikin kasashen duniya da ake yaki a cikinsu.

@facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments