Sunday

Home › › Jigawa Da Saudiyya Za Su Hada Gwiwa Kan Ilmi Da NomaGwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta hada gwiwa da Masarautar Saudiyya domin bunkasa ilimi da noma a jihar baki daya. Gwamnan jihar ta Jigawa, Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar masarautar ta Saudiyya a Dutse cikin makon da ya gabata. Gwamnan ya ce, bayan samun labarin sabuwar jami’ar da masarautar ta Saudiyya ta bude, gwamnatin Jihar Jigawa na da sha’awar masarautar ta baiwa dalibai ‘yan asalin jihar guraben kara karatu musamman a fannonin da suka shafi kimiyya da fasaha da kuma likatanci da dai sauran fannoni da dama. Haka kuma ya bayyana cewa, Jihar Jigawa Allah ya albakace ta da kasar noman alkama wadda yawanta ya haura hekta 200,000 don haka suna gayyatar masarautar ta Saudiyya domin zuwa ta zuba jarinta a wannan fannin.Gwamna Badaru ya kuma tallafa wa masarautar ta Saudiyya lafiyayyun dabbobin da Allah ya huwace wa jihar domin amfani a matsayin nama ga masarautar. Shi kuwa a nasu bangaren, wakilin kasar ta Saudiyya, Malam Ibrahim Kabir ya bayyana cewa sun ziyarci wannan jiha ne domin karfafa alakar dake tsakanin masarautar da jihar ta Jigawa. Haka kuma ya sha alwashin fadada alakar tasu domin amfanin kowanne daga cikinsu.
No comments:
Write Comments