Wednesday

Home › › Karyane Donal trump bai kirawo Buhari ba | 'kungiyar igbo
Kungiyar Igbo tace kiran da Trump yayiwa Buhari farfaganda ne .
- Kungiyar Dream Imo ta yarda cewa daukar kiran Donald Trump da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi laifi ne da ya kamata a tsige shi - Kungiyar tace tunda an kaddamar da shugaban kasa mai rikon kwarya, Farfesa Yemi Osinbajo, a kundin tsarin mulki shi yakamata ya dauki irin wannan kira Dream Imo,

wata kungiya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya ta kaddamar da cewa bai dace shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kira Muhammadu Buhari ba kamar yadda aka ruwaito. Wannan yazo ne duk da rahotannin dake cewa Trump ya tabbatar da kira a tsakanin shugabannin kasar guda biyu.

A wata sanarwa daga shugaban ta, Emmanuel Nzenwa, kungiyar tace bata yarda da cewan Buhari dake hutun ganin likita a kasar waje zai iya daukan kira daga Trump ba musamman ma tunda yana kasar waje ne.

Ya kuma bayyana cewa shugaban kasa mai rikon kwarya Yemi Osinbajo ne yakamata ya dauki wayar tunda ba wai kira da ya shafi shugabannin guda biyu bane. Ya bayyana cewa ko CNN da ruwaito ci gaban ta ce daga bakin Femi Adesina ne, kakakin shugaban kasa Buhari. Kungiyar tayi korafin cewa Buhari yaki yin jawabi ga mutanen Najeriya game da rade-radin mutuwarsa kuma yaki haduwa da yan Najeriya a birnin Landan.
No comments:
Write Comments