Tuesday

Home › › Kenya ta bada umurnin tsare shugabanin kungiyar lauyoyin kasar 7.
Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta.


Wata Kotu a kasar Kenya ta bada umurnin tsare shugabanin kungiyar lauyoyin kasar 7 a gidan yari saboda kin janye yajin aikin makwanni 10 da ya jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali. Mai shari’a Hellen Wasilwa ta yanke hukuncin ne bayan shugabanin lauyoyin sun ki mutunta umurnin janye yajin aikin da suka fara saboda kin amincewa da Karin kashi 40 na albashin da gwamnatin ta musu. Nan ta ke aka tasa keyar jami’an guda bakwai cikin mota sanye da ankwa a hannayen su zuwa gidan yari.

Lauyan su ya ce za su daukaka kara.
©facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments