Tuesday

Home Ko Kasan Abin da gwamntin Buhari ke shirin yi wa 'Yan Neja-DeltaGwamnatin tarayya na wani shiri a
Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur
Za a kashe fiye da Dala Biliyan 20 domin
wannan aiki.
Fiye da mutane 250,000 za su samu aiki
idan har aka kammala aikin
Gwamnati na shirin wani aiki a yankin Neja-
Delta.


Gwamnatin tarayya na shirin gina wani
wurin aiki a Yankin Neja-Delta da zai
taimakawa Yankin ya kuma samar da
ayyuka akalla 250,000. Mukaddashin
shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ya
bayyana haka.
Wannan wuri da za a gina dai zai kai
tsawon kilomita 60 inda za a rika
ayyukan mai. Idan har an ci ma
wannna buri za a rika samun sinadarin
methanol da sauran sinadarai da ake
samu daga danyen mai har ma da
sinadarin hada takin zamani.


Irin aikin da Gwamnati ke shirin yi a yankin
Neja-Delta.

Farfesa Osinbajo yace duk wannan yana
cikin muradun shugaba Buhari na
tallafawa Yankin Neja-Delta mai arzikin
man fetur. Za dai ayi wannan aiki ne a
Garin Ogidigben da ke Jihar Delta.
Mutanen kasar Sin da Larabawa ne dai
ake sa ran za su yi wannan aiki.
Yanzu haka dai Farfesa Osinbajo ke rike
da Najeriya ya kuma yi ayyuka tafiyar
shugaba Buhari na a-zo-a-gani. Kadan
daga ciki su ne sauyi da aka gani a
tsare-tsaren harkar kudin kasar daga
CBN. Farfesa Osinbajo kuma ya shiga
lungunan Neja-Delta domin kwantar da
rikicin da ke Yankin.No comments:
Write Comments