Monday

Home Ko kasan Mutane 4n Da suka hana kowa ganin shugaba Buhari yanzu haka?
Babu dai wanda ya isa ya ga shugaban
kasar sai ta hannun su…Idan ba Hajiya Aisha Buhari ko Osinbajo
ba babu wanda ya isa ya ga Buhari

A wani bincike da Jaridar Punch tayi an
gano cewa wasu manyan kusoshi ne
suka katange shugaba Buhari inda suka
hana kowa ya gana da shi. Yanzu haka
dai shugaba Buhari yana Landan kuma
babu wanda ya isa ya je kusa da shi sai
ta hannun wadannan mutane.

Ciki dai akwai shugaban Ma’aikatan
gidan gwamnati da kuma wani mai
taimakawa shugaban kasar watau Abba
Kyari da kuma Tunde Sabi’u. Punch
tace idan dai har ba Hajiya Aisha
Buhari ko Mataimaki Yemi Osinbajo ba,
babu wanda ya isa ya ga shugaba
Muhammadu Buhari kai tsaye.

Sannan kuma Alhaji Mamman Daura,
duk ganawar da Buhari yayi da Jama’a
kwanaki a Landan, Mamman Daura
yana biye ko da dai bai da wani
mukami a gwamnati, sai dai ‘dan uwa
ne kuma na kusa da Buhari.

Akwai kuma wani Sarki Aba wanda ko
da ba a san sa ba, yana cikin wadanda
suke bada dama a gana ko ayi waya da
shugaba Muhammadu Buhari.
No comments:
Write Comments