Thursday

Home › › Kotu za ta yi shari'a ga mutumin da ya kona Alkur'ani tare da yada hotunansa .
Kotu a kasar Denmak za ta yi shari'a tare da yanke hukunci ga wani mutum da ya kona Alkur'ani Mai Tsarki a lambun da ke bayan gidansa tare da yada hotonsa a shafin sada zumunta na Facebook.

Kotu a kasar Denmak za ta yi shari'a tare da yanke hukunci ga wani mutum da ya kona Alkur'ani Mai Tsarki a lambun da ke bayan gidansa tare da yada hotonsa a shafin sada zumunta na Facebook.
Daya daga cikin masu gabatar da kara na kasar da ke garin Viborg Jan Reckendorff ya ce, dan kasar ta Denmak mai shekaru 42 ya kona Alkur'ani a lambun da ke bayan gidansa tare da yada hotuna a shafin Facebook a ranar 27 ga watan Disamban shekarar 2015.

Za a yi wa mutumin hukunci karkashin sashen na 140 na dokokin kasar da suka hana cin mutunci da batanci ga wani Addini.
Ana hasashen za a iya yanke masa hukuncin dauri da ya kai watanni 4.
Ba a bayyana ranar da za a fara zaman shari'ar ba wanda kotun Aalborg za ta saurara.
No comments:
Write Comments