Saturday

Home › › Kungiyar ‘yan uwa Musulmi na shirye-shiryen kai munanan hare-hare a Najeriya .
Gwamnatin Najeriya a ranar Juma’ar nan ta gargadi jama’ar kasar bisa shirin kungiyar ‘yan uwa Musulmi wadda reshen Boko Haram ce da ke jihar Kogi da ke tsakiyar kasar inda suke shirin mallakar wasu manyan makamai masu hatsari don kai hare-hare munana.

A wata sanarwa da aka fitar a Abuja babban birnin Najeriya, ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa, an samu bayanan sirri na wani waje da kungiyar ke samar da makamai da kananan bama-bamai ga mambobinsu.

An gano cewa, wani dan kungiyar me koyon samar da bam Usman ya tafi kasar Libiya don yin yaki tare da Daesh wanda ake tunanin ya sake dawo wa Najeriya don ci gaba da samar da abubuwean fashewa ga kungiyar. Lai Muhammad ya kuma ce, kungiyar na shirin mallakar makanan roka, kuma suna shirin fasa gidajen yari na Najeriya don kubutar da mambobinsu da suka hada da wani da ake kira Bilyaminu wanda ke gidan kurkukun Kuje kuma kwararre wajen hada bam.©facebook/hausapost28
No comments:
Write Comments