Thursday

Home › › 'Kungiyoyin 'Kwadago sun yiwa Buhari Kashedi.Kungiyoyin kwadago da suka hada da Nigerian Labour Congress (NLC) da kuma Trade Union Congress (TUC) sun rubuta ma gwamnatin tarayya takarda suna mai kashedin ta da wata sabuwar kungiya da ta kunno kai.

Takardar wadda aka aike wa gwamnati tun ranar 19 ga watan Janairu tana dauke ne da Bayanin cewa akwai fa wasu yan bani-na-iya da suke kokarin kafa wata kungiyar kwadago wadda kuma shugabannin NLC da TUC din suka sa wa hannu watau Ayuba Wabba da Bobboi Kaigama wadda kuma suka aikewa ministan kwadago Dr. Cris Ngige.

Takardar da suka aikewa ministan sun bayyana cewa wasu ne da basu samu mulkin kungiyoyin ba suke kokarin ganin sun bata ruwa-ba-don su sha ba ta ko wane fanni.
Ku same mu a twitter @hausapost28
No comments:
Write Comments